HKI Ta Nuna Damuwarta Da Jibge Sojojin Da Gwamnatin Masar Ta Yi A Yankin Sina

Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI. Tun

Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI.

Tun bayan da gwamnatin HKI ta gama lalata makaman gwamnatin kasar Siriya bayan ta taimaka ta kawo dan Daesh kan kujerar shugabancin kasar ta Siriya, kuma ta bayyana cewa yankunan da ta mamaye a kasar Siriya sun zama HKI ne har abada.take nuna damuwa da kasar Masar.

Banda haka mun ga yadda sabon shugaban kasar ta Siriya  Julani ya yi shiri da bakinsa a kan mamayar da HKI takewa kasar Siriya da kuma yadda ta kai hare-hare fiye da dubu guda kan kasar tana lalata makamanta, ko wa ya fahinci cewa, siriya ta gama yawo,. Kuma ba zata taba daga ko tsinke a gaban HKI ba.

Tashar talabijin ta Presstv ba ce, a halin yanzu hankalin yahudawa ya koma kan kasar Masar, wacce take ganin bangare na HKI kuma kasar tana iya zama matsala gareta, duk tare da nasarorin da ta samu ya zuwa yanzu na mamayar kasashen larabawa.

Tsohon babban haffsan sojojin HKI Herzi Halevi ya fito fili ya na cewa suna cikin damuwa dangane da kasar Masar. Don ta sami ci gaba sosai a bangaren mallakan makamai  na zamani.

Ya kuma kara da cewa, a shekara ta 2011 da aka yi juyin juya halin na yanuwa musulmi, wato Muhammad Mursi sun ji tsaro, amma sun dan numfasa bayan an kauda Mursi. Sai dai a halin yanza akwai barazana na kara karfi a bangaren kasar ta  Masar, musamman bayan yakin 7 ga watan Octoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments