Hukumar da take tafiyar da yankin na Gaza, ta sanar da hakan sannan ta kara da cewa; A shekaran jiya Asabar ma dai sojojin mamayar sun kai wani hari akan Asibitin “Kamal-Adwan” da yana cikin kadan da su ka rage sun aiki a Gaza. Makwanni biyu a jere kenan sojojin na Isra’ila suna kai wa wannan asibitin hari ta hanyar amfani da jiragen sama da kuma manyan bindigogi daga kusa.
Hukumar ta Gaza ta kuma bayyana cewa a cikin watanni 13 daga yakin, sojojin HKI sun kashe likitoci da ma’aikatan jiyya 1000, sannan kuma sun kama wasu da adadinsu ya kai 310. Bugu da kari sojojin na HKI sun hana shigar da kayan aiki da magani acikin asibitocin yankin, ko kuma fitar da masu jiyya zuwa asibitocin kasashen waje, domin yi musu magani.
Tun farkon yakin da HKI ta shelanta akan Gaza, ta rika kai wa asibitoci, likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya hare-hare a matsayin manufar jefa Falasdinawa cikin tsoro da razani.
A shekarar da ta wuce , HKI ta kai hari akan asibitin “Ma’amadani” dake Gaza wanda a lokaci daya ya yi sanadiyyar shahadar mutane 500.
Daga fara yakin Gaza zuwa yanzu, adadin Falasdinawa da su ka yi shahada sun kai 43,000, wadanda kuma su ka jikkata sun haura 100,000.
A jiya Lahadi ma dai sojojin HKI sun kashe wasu kananan yara biyu a garin Ya’abad, dake yammacin Jenin a Arewacin kogin Jordan.
Kamfanin dillancin labarun “Wafa” na Falasdinawa ne ya nakalto labarin yana mai kara da cewa; Sojojin mamayar sun kutsa cikin garin ne ta gabashinsa, lamarin da ya haddasa taho mu gama a tsakaninsu da samarin garin.