Sojojin HKI sun kai falasdinawa akalla 72 ga shahada a safiyar yau Litinin, daga cikinsu har da yara kanana da kuma wadanda suke jiraran a basu taimakon abinci a cibiyoyinsu a cikin Gazzar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a yau litinin a Gaza sojojin HKI sun kashe Falasdinawa a wurare da dama a gaza. Labarin ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka ji ciwo zuwa asbitin Al-Ahli. Bayan haka yahudawan kai kai hare-hare a yankin Zaitun da kuma kasuwar zawiyya.
Labarin ya kara da cewa baba gadaje a Asbitin don haka zaka ga wadanda suka ji ciwon kwance a kasa. Har’ila yau labaran sun bayyana cewa mafi yawan wadanda sojojin yahudawa suka kashe sun kashesu ne a cibiyar bada agajin gaggawa wanda Amurka da HKI suka tsara don kashe mafi yawan adadi da zasu iya kashewa a Gaza, bayan sun hanasu abinci na kimani watanni 3.
A karshen watan mayun de ya gabata ne Amurka tare da yahudawan suka bullo da wannan tarkon don kara kashe Falasdinawa bayan sun hana shigo da abinci yankin. Suna kashesu ne a dai-dai lokacinda suke cikin tsananin yunwa. Inda ya zama masu dole su je su nemi abinci duk inda yake.