HKI Ta Kai Sabbin Hare-Hare Kan Tashar Jiragen Sama Na Birnin San’a

Majiyoyin labarai a kasar Yemen sun bayyana cewa HKI ta kai hare-hare a kan tashar Jiragen sama a birnin San’aa inda a wannan karon suka

Majiyoyin labarai a kasar Yemen sun bayyana cewa HKI ta kai hare-hare a kan tashar Jiragen sama a birnin San’aa inda a wannan karon suka lalata hanyar tashin jiragen sama a tashar.

Tashar talabijan ta Al-manar ta kasar Lebanon ta kanalto majiyar HKI tana tabbatar da wannan labarin.

Tashar radio ta HKI ta nakalto ministan yakin HKI Yasra’il Katz yana tabbatar da wannan labarin ya kuma kara da cewa hare-haren ta sama sun wargaza wani bangare na tashar jiragen sama na birnin, sannan ya lalata jirgin sama tilo wanda ya rage a tasahr jiragen.

Hakama tasha ta 12 ta HKI ta nakalto Katz yana cewa jiragen yaki fiye da 10 ne suka yi aikin hare-hare a kan tashar jirage na Sa’aa.

Kafin haka dai sojojin kasar Yemen a jiya Talata ma sun cilla makamai masu linzami samfurin Bilistic zuwa kan  tashar jiragen sama na Bengerion don tallafawa mutanen Gaza wadanda HKI take kashewa da yunwa da kuma wuta ta ko ina.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments