HKI ta kai hare-hare kan wurare 5 a kudancin kasar Lebanon a jiya Alhamis.
Tashar talabijin Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa kafin hare-haren yahudawan sun bada sanarwan cewa zasu kai hare-hare kan warare uku a gudancin kasar ta Lebanon a jiya Alhamis kuma sune Meis al-Jabal, Debbine, da kuma Kafar Tebnit.
Mai aikawa tashar talabijin ta kasar Lebanon rahoto daga kudancin kasar ta bayyana, amma a lokacinda ta fara kai hare-hare jiragen yakin da ake sarrafawa daga nesa, suka fara shawagi a kan wadan nan wurare, suna ayyukan leken asiri. Sannan bayana wani lokacin makaman Drones suka ketasararin samaniya kasar Lebanon suka kai hare-hare har guda biyu a kan garin Meisal-Jabal, inda ya jiyamutum guda rauni.
Yar rahoton Al-mayadden a kudancin Lebanon ta bayyana cewa bayan haka jiragen ‘Drones’ su sake shigowa kudancin kasar suka kai hare-hare a wannan karon kan gidajen mutane a Kafar Tebnit da lardin Nabatieh. Sun kumakaihare-hare kan garin Debbine a can kuryar kudancin kasar.