Sojojin mamayar HKI sun kai sabbin hare-hare a wasu yankuna na gabashin kasar Lebanon, adaidai lokacin da take ci gaba da kai wa yankin yammacin kogin Jordan wasu gare-haren.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; Sojojin mamayar sun kame Falasdinawa 5 a garin al-Khalil dake kudancin yammacin kogin Jordan. Haka nan kuma sun kama wasu Falasdinawa 8 a garin Nablus.
A garin Bireh da wasu yankuna na Ramallah, sojojin mamayar sun kai wasu hare-haren a yau Laraba.
A cikin watannin bayan nan, sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinwa 79 a cikin yankin yammacin kogin Jordan, tare da tilastawa mazaunan gidajen kusan 40,000 yin hijira.
A ranar 22 ga watan Maris ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a garuruwan Lebanon da su ka hada, Nabi Shit, Hermel, da wasu garuruwan da suke a yankin Bika. Haka nan kuma sun kai wasu hare-haren a garin Deir Qanun.
Tun daga fara yaki akan Gaza, sojojin HKI sun kashe Falasdinawan da sun haura 50,000, yayin da wani adadin da ya kai mutane113,000 su ka jikkata.
A can yankin Gaza ma, sojojin na HKI suna cigaba da kai hare-hare wanda ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama.
Hare-haren na sojojin mamaya ya shafi garin Khan-yunus dake kudancin Gaza, haka nan kuma a garin Rafaha dake kan iyaka da kasar Masar.
Da safiyar yau Laraba kadai Falasdinawa 11 ne su ka yi shahada, daga cikinsu da akwai kananan yara 5.