HKI Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kudancin Kasar Lebanon

A dai-dai lokacinda jiragen yakin HKI suke ci gaba da kai hare-hare kan mutanen kudancin Lebanon sannan suka ci gaba da keta hurumin yarjeniyar da

A dai-dai lokacinda jiragen yakin HKI suke ci gaba da kai hare-hare kan mutanen kudancin Lebanon sannan suka ci gaba da keta hurumin yarjeniyar da aka cimma da kungiyar Hizbullah, tana kashe mutanen kasar Lebanon. A wani bangare kuma Sojojin UNIFEL suna fuskantar turjiya daga mutanen kudancin kasar ta Lebanon.

Jaridar Arba News ta kasar Saudia ta bayyana cewa mutane a yankin sun hana sojojin UNIFEL shiga wasu unguwanni a yankin don gudanar da bincike a cikin gidajen mutane.

Labaran da suke fitowa daga irin wadannan yankuna sun nuna cewa muatne sun hana sojojin nUnufel shiga wasu unguwanni, sai sun kawo sojojin kasar Lebanon .

Sojojin sun dage saisun  shiga amma mutane sun hansu shiga a sannane suka fara amfani da teas gas ko iska mai sa hawaye don tarwatsa su. Wannan bai yi amfani ba.

Gwamnatin kasar Lebanon ta bukaci a tsawaita lokacin wanzuwar sojojin UNIFEL a kudancin Lebanon amma ta bayyana a fili sojojin suna aiki wa HKI da Amurka ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted