Kafafen watsa labarun HKi sun ambato jami’an soja na cewa, mayakan Hamas sun sake gina kansu ta hanyar daukar dubban mayaka, kuma suna nan a arewacin Gaza ba su fita daga ciki ba.
Kafafen watsa labarun na HKI sun kuma kara da cewa; mayakan da kungiyar take da su a yanzu, sun rubanya mayakanta na baya, kafin barkewar yaki, kuma kungiyar ta koyi darussa daga yaki da sojan kasa na Isra’ila a baya.”
Jaridar “Badiot Ahranot” wacce ta dauki labarin ta kuma ce; Har yanzu Hamas ba ta fito da dukkanin mayakanta a filin daga ba, da adadinsu ya kai 30,000, kuma tana ba su albashi ta hanyar kudaden harajin da take karba.
Wani sashen na bayanin kafafen watsa labarun ‘yan sahayoniyar ya kunshi cewa; Hamas ta sake dawo da harkokin tafiyar da sha’anin yankin na Gaza domin sake gina karfinta na soja da tattalin arziki.