HKI: Barazana Ba Ta Tasiri Akan Hamas

Kafafen watsa labarun HKI sun ce; Barazanar da ake yi wa kungiyar Hamas ba ta wani tasiri a gare ta. Kafafen watsa labarun na HKI

Kafafen watsa labarun HKI sun ce; Barazanar da ake yi wa kungiyar Hamas ba ta wani tasiri a gare ta.

Kafafen watsa labarun na HKI suna yin tambaya akan yadda Hamas din take isar da sakwanni a fakaice ga Isra’ila a yayin bikin mika fursunoni da take shiryawa.

Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; A cikin wannan yanayi mai tsanani da ake ciki, ko wane sako ne kungiyar ta Hamas take son isarwa ta hanyar shirya biki a yayin sakin fursunoni?

Shi kuwa mai yi tashar sharhi, Ohad Hamu, ya ce kungiyar ta Hamas ta isar da sako da harshen Hebrew da take mahana da Isra’ilawa, sai kuma turanci da take Magana da gwamnatin Amurka, da hakan yake nufin kin amincewa da shirin Donald Trump.

Ita kuwa tashar talabijin ta 13: cewa ta yi  Hamas ta yi watsi da dukkanin  sakwannin  da Isra’ila  take aike mata, kuma ko kadan ba ta damu da barazanar da ake yi ma ta ba.

Har ila yau tashar talabijin ta 12; ta ce, hotonnin da suke fitowa daga Gaza suna nuni da cewa, har yanzu Hamas ce take iko da yankin.

Shi kuma tsohon Fira ministan HKI Ehud Barack cewa ya yi; rashin tsayayyar manufa ta gwmanatin Netanyahu ne ya sa har yanzu Hamas din yake ci gaba da iko da Gaza. Ya kuma kara da cewa, ba ta hanyar kashe shugabannin Hamas ne za a kawo karshenta ba, sai dai ta hanyar samar da wadanda za su maye gurbinta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments