Ministan tsaron HKI Israel Katz ya bayyana cewa gwamnatin HKIba zata bar a kafa kasar Falasdinu ba, saboda hakan barazana ce ga samuwar HKI.
Israek Kazt ya bayyana haka ne a lokacin ganawar jami’an gwamnatin HKI da tawagar kasar Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a taron su da tawagar kasar ta Amurka a yau. Ya kuma kara da cewa abubuwan da HKI ta sa a gaba sun hada da ganin kasar Iran bata mallaki makaman Nukliya ba, da shafe kungiyar hamas, sakin fursinoni a hannun Hamasa da kuma samar da huldar jakadanci da kasar Saudiya.
Wasu kafafen yada labarai sun nakalto wasu manya manyan jami’an sojojin kasar suna tunanin dakatar da tsagaita wuta da suka kulla da Hamas. Banda haka suna ganin shawarar shugaba kasar Amurka Donal Trump n araba gaza da Falasdinawa ne kawai zai tabbatar da wanzuwar HKI.
Kafin haka dai Banyamin Natanyahu ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa Falasdinawa suna da damar su bar Gaza su je inda suka ga dama, idan sun bukaci hakan, amma idan bas u yi ba, to mai yuwa a kashesu gaba daya.