A bayanan da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Lahadi ta bayyana hare-haren da ta kai wa cibiyoyin soja da sansanonisu na sama, kasa da ruwa a lokuta mabanbanta.
Birnin Tel Aviv yana cikin wuraren da Hizbullah ta kai wa hare-hare har sau 3 da makamai masu linzami masu cin dogon zango. Har ila yau yankin Khudaira dake gaba da Tel Aviv, ya fuskanci hari daga kungiyar ta Hizbullah.
Kafafen watsa labarun HKI sun kuma ambaci cewa sau 500 jiniyar gargadi ta kada a fadin Haramtacciyar Kasar, sanadiyyar hare-haare daga Lebanon.
Har zuwa marecen jiya kungiyar ta Hizbullah ta harba makamai masu linzami 340 a garuruwa mabanbanta na ‘yan sahayoniya.
Hare-haren da Hizbullah ta kai wa HKI a jiya Lahadi kadai sun kai sau 42. Har ila yau mayakan na Hizbullah sun tarwatsa motocin “Mirkava” 4 a kudancin Lebanon, tare da kashe da jikkata sojojin da suke cikinsu.
A wani daga cikin bayanan da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana cewa; Idan Isra’ila ta kai wa Beirut Hari, to Tel Aviv Za Ta Fuskanci Hari.”
Hare-haren na jiya dai sun zo ne, kwanaki kadan da su ka gabata babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya sanar da cewa daga yanzu duk lokacin da HKI ta kai wa Beirut hari, to za su mayar da martani ta hanyar kai wa Tel Aviv hari.