Hizbullah ta yi Allah wadai da harin Amurka da Birtaniya a kan Yemen

Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Birtaniya suka kai kan kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da

Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Birtaniya suka kai kan kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama a daren jiya Asabar.

Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da wadannan hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya suka kai kan wasu unguwanni a Sanaa babban birnin kasar, da kuma wasu larduna da dama, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Bayanin ya kara da cewa, “Wannan zaluncin ya zo ne a matsayin wani yunkuri na murkushe wannan al’umma mai girma mai tsayin daka wajen ci gaba da nuna goyon bayanta ga al’ummar Gaza da kuma ci gaba da nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu.”

Sanarwar ta yi nuni da cewa, hare-haren da ake kaiwa fararen hula da muhimman ababen more rayuwa a kasar Yaman, ya sake bayyana hakikanin gaskiya da mummunar fuskar gwamnatin Amurka, wadda ke aiwatar da ayyukan cin zarafi ga kasashen da ke adawa da manufofinta a yankin da ma duniya baki daya.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bayyana harin da Amurka ta kai birnin San’a a matsayin laifin yaki da kuma keta dokokin kasa da kasa, wanda kuma ya yi dai-dai da irin hare-haren Isra’ila a kan Gaza, Siriya, kuma Lebanon.

 Hizbullah ta ci gaba da cewa: Al’ummar kasar Yemen masu tsayin daka, wadanda suka rubuta kasidu na jarumtaka tare da jinin shahidansu na goyon bayan al’ummar Palastinu da Gaza, kuma suka tsaya tsayin daka a karkashin jajircewar  shugabanninsu, irin wannan al’umma ba za su ja da baya ba wajen tinkarar wannan zalunci na makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments