Kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta kai hari kan wani sansanin sojin Isra’ila a yankunan arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye.
A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar a safiyar yau Litinin ta ce, mayakanta sun harba makaman roka a kan sabuwar hedikwatar sojin Isra’ila bataliya ta 146 da aka kafa a Giaton.
Ta kara da cewa an kai harin ne a matsayin martani ga hare-haren da Isra’ila ta kai kan yankunan fararen hula a kudancin kasar Lebanon, musamman a garin Maaroub.
Sanarwar ta ce, “Mayakan kungiyar a yau Litinin, 12-08-2024, sun kai hari a sabuwar hedikwatar kuma sun samu nasarar tawrwatsa wasu muhimman sassa na hedkwatar da sojojin Isra’ila da suke ciki.
A cewar kungiyar Hizbullah, babbar manufar dukkanin wadannan hare-hare it ace taimaka ma al’ummar Gaza kan kisan kiyashin da yahudawa ke yi musu babu kakkautawa, kuma Hizbullah ba zata dakatar da hare-harenta kan sojin Isra’ila ba har sai sun daina kai hari kan al’ummar zirin Gaza.
A cewar kafofin yada labaran gwamnatin Isra’ila, tsarin tsaron sararin samaniya na Iron Dome na Isra’ila ya kasa tare yawancin makamai masu linzami na Hezbollah.
Harin ya haddasa wata babbar gobara a yammacin Galili da ke arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye.