Shugaban kungiyar Hizbullah Sheihk Naim Qassem ya ce za a ci gaba da yin shawarwari muddin aka cimma abubuwan da suka hada da tsagaita bude wuta ta dindindin da kuma kiyaye hurimin kasar Lebanon.
Ya kara da cewa, Hizbullah a shirye take don yaki mai tsawo.
“Idan tattaunawar ta gaza, za mu ci gaba da fafatawa, muna da iyawa kuma za mu jure,” inji Sheihk Qassem a jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo da yammacin yau Laraba.
Shugaban Hezbollah ya sha alwashin mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar Labanon, yana mai cewa wannan ramuwar gayya za ta kasance a cikin “zuciyar Tel Aviv”.
Ya kara da cewa kungiyar na da tsayin daka da juriya kuma mayakanta na iya shiga ko’ina tare da fatattakar sojojin Isra’ila.