Hizbullah: Ba Za Mu Taba Ajiye Makamanmu Ba

Mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hizbullah Mahmud Kumadhi ya bayyana cewa: Bayan da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kasa murkushe gwgawarmaya a Falasdinu, yanzu ta

Mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hizbullah Mahmud Kumadhi ya bayyana cewa: Bayan da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kasa murkushe gwgawarmaya a Falasdinu, yanzu ta kuma kai wa kudancin Lebanon hare-hare.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto Mahmud Kumatiy ana cewa; Abinda ‘Yan mamaya suke yi, shi ne kokarin shimfida ikonsu a cikin wannan yankin na yammacin Asiya baki daya, sai dai hakan ba za ta faru ba.

Muhammad Kumadhi ya kuma jaddada cewa; ko kadan Hizbullah ba za ta taba ajiye makamanta ba, ko kuma ta kauce daga kan godaben gwagwarmaya komai tsananin matsin lambar Isra’ila.”

Mataimakin shugaban ofishin siyasa na Hizbullah ya kuma ce; Hzibullah kungiyar gwgawarmaya ce ta kasar Lebanon, kuma ta musulunci,aikin da yake gabanta shi ne kare kasar Lebanon.”

Haka nan kuma ya ce; Ba ma kore cewa muna da alaka da Iran,ba kuma za mu taba yanke alakarmu da ita matukar tana ci gaba da taimaka mana da mu’amala da mu cikin girmamawa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted