Hezbulla: Iran Ce Babbar Mai Goyon Bayan Al-Ummar Falasdinu

Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk

Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya.

A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya bayyana cewa ware ranar jumma’a ta karshe na watan Ramadan wata hikima ce ta jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ruhullah Alkhomaini(q) wanda ya dace da hakan kan musulmi a kan wannan al-amari. Kuma tare da yardarm All…ana ci gaba da samun nasara a kan wannan manufar.

Sheikh Kasim ya kara da cewa duk tare da gagarumin taimakon da HKI take samu daga kasashen yamma musamman Amurka wannan ba zai hana yunkurin yentar da kasar Falasdinu samun nasara ba, musamman ganin yadda al-amarin kasar Falasdinu ya zama al-amari na farko a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments