Babban Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana a wani jawabi da ya yi da aka watsa ta gidan talabijin a wannan Alhamis cewa, ‘yan kasar Labanon sun yi sadaukarwa, sun bayar da shahidai da wadanda suka samu raunuka a tsawon kwanaki 64 da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kwashe tana tana luguden wuta a kan gidajen Jama’a da kaddarorinsu, da cibiyoyi, gami da sauran wurare na rayuwar jama’a, amma duk da hakan sun juriya ta hanyar hakuri, dagewa, da kuma dogaro ga Allah.
Dangane da yarjejeniyar dakatar day akin ‘Isra’ila ta karya yarjejeniyar har sau fiye da 60.
Sheikh Qassem ya jaddada cewa kungiyar Hizbullah za ta daure, kuma za ta kara samun ci gaba.
Sannan kuma ya jaddada cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbullah ta amince da ita, tana aiki a matsayin tsarin aiwatar da kuduri mai lamba 1701.
“Yarjejeniyar da muka amince da ita ita ce wadda ta shafi kudancin kogin Litani,” in ji shi, ya kuma kara da cewa dukkanin sauran batutuwan da suka shafi kuduri mai lamba 1701 “suna da nasu tsarin,” wanda ya hada da dawo da iyakokin kasar ta Lebanon cikin wa’adin da aka kayyade.
Dangane da tashe-tashen hankula na baya-bayan nan a Siriya, Sheikh Qassem ya ce, hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a Siriya, sakamakon gazawarsu ne a Gaza da kuma gazawar da suka yi na hankoron rusa kasar Siriya a baya.
Dangane da haka, ya sha alwashin cewa, “Mu a kungiyar Hizbullah, za mu tsaya tsayin daka tare da Syria wajen dakile manufofin wuce gona da iri a kanta.”
A cikin sakon da ya aike wa kasashen Larabawa, ya jaddada cewa, “Ku sani cewa duk wata nasara da “Isra’ila” za ta samu, asara ce a gare ku, ba kawai ga Falasdinu, Siriya da Labanon ba, kuma hakan zai yi tasiri ga kasashenku.
Ya kara da cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda na da niyyar kawar da kasar Siriya daga matsayinta na bangaren gwagwarmaya da yaki da manufofin ‘yan mulkin mallaka a yankin, zuwa matsayin da ya dace da manufofin Isra’ila.