Hezbollah ta tabbatar da shahadar babban kwamanda Ibrahim Aqil a harin da Isra’ila ta kai

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da shahadar  babban kwamanda Ibrahim Aqil a wani harin da Isra’ila ta kai. A cikin wata sanarwa da

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da shahadar  babban kwamanda Ibrahim Aqil a wani harin da Isra’ila ta kai.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar a daren Juma’a ta yi matukar yabo jinjina ga kwamandanta da ya yi shahada.

Kungiyar gwagwarmayar ta ce “fitaccen jagoran jihadi, Hajj Ibrahim Aqeel , ya shiga sahun ‘yan uwansa shahidai, manyan jagororin da suka gabace shi.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Rayuwarsa ta kasance gaba dayanta  sadaukarwa ce ba tare da gajiyawa ba, wanda ke nuni da ruhinsa na  jihadi, juriya, da jajircewa wajen fuskantar lamurra masu tsanani a tafarkin kae gaskiya.”

A jiya Juma’a ne Isra’ila ta kai wani hari a yankin kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar ta Lebanon, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar mutane da dama da kuma jikkata, hakan ya zo ne kwanaki biyu bayan harin na’urorin sadarwa da Isra’ila ta kai a kasar, wanda shi ma ya yi sanadiyyar shahadar wasu da kuma jikkatar mutane da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments