Search
Close this search box.

Hezbollah: Ba Zamu Ji Tsoro Ba Kuma Ba Zamu Jada Baya Ba

Shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata ji tsoro ba kuma ba zata jada bayana ba saboda

Shugaban majalisar zartarwa ta kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata ji tsoro ba kuma ba zata jada bayana ba saboda hare haren da HKI ta kai kan na’urorin sanarwan na kungiyar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyed Hashem Safieddine, yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa kungiyar tana shirin daukar fansa kan HKI saboda cutar da mutanen kasar Lebanon da ta yi.

Sayyed Dafieddine ya bayyana haka ne a lokacinda yake halattar Jana’izar wasu daga cikin yayan kungiyar wadanda suka yi shahada sanadiyyar hare haren HKI na baya bayana nan.

Babban jami’in kungiyar ta Hizbullah ya yi kira ga yayan kungiyar da su yi aikin don tallafa kungiyar kan makiyanta, da kuma taimaka mata don ganin ta sami nasara ta karshe.

Syyed Safieddine ya bayyana haka ne kwana guda bayan hare haren HKI ta kai kan na’urorin sadarwa na lantarki wanda ake kira ‘pager’, wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 12 da kuma jikata wasu kimani 3,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments