Kakakin rundunar “Hashd al-Shaabi” ya jaddada cikakken shirin sojojin Iraki na kare iyakokin kasar da sauran yankunan kasar, sannan ya jaddada cewa ba za a taba maimaita irin yanayin da kasar ta shiga a hannun ‘yan ta’adda na ISIS a shekarar 2014 ba.
Shafin middle East ya bayar da rahoton cewa, rundunar Hashd al-Shaabi ta tabbatar wa al’ummar kasar cewa ba za a taba samun irin wannan yanayin na shekarar 2014 a kasar ba.
Moayed al-Saadi, kakakin dakarun Hashd al-Shaabi, a wata hira da jaridar “Al-Sabah” ta kasar Iraki, a daidai lokacin da ake samun saurin sauye-sauye cikin sauri a kasar Siriya, ya bayyana cewa: Dukkanin matakan da dakarun Hashd al-Shaabi suka dauka suna cikin tsarin shawarwarin Mohammad Shi’yaa Al-Sudani babban kwamandan sojojin kasar da kuma Faleh Al-Fayyad shugaban rundunar Popular Mobilisation Organisation, ko kuma Hashd al-Shaabi, inda suke magana akan bukatar karfafa shingen kan iyaka na Iraki da Siriya don hana maimaita abin da ya faru a cikin 2014.
Dakarun sojin kasar Iraki da Hashd al-Shaabi, sun tabbatar da cewa yiwuwar faruwar irin wadannan al’amura ba abu ne da za a bari ba.
Kakakin Hashd al-Shaabi ya bayyana cewa: Manufar Tafiyar Falah al-Fayad shugaban wadannan dakaru zuwa lardin Nainawa a haƙiƙa ita ce don isar da saƙo mai ƙarfafawa ga Hashd al-Shaabi cewa dakarun sun shirya tsaf don tallafawa ƴancin kasar Iraki da shirye shiryen kasancewa a fagen daga bisa ga umarnin babban kwamandan rundunar soji ta kasar Iraki.