Mali: Harin Jirgin Yakin Sojoji Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 18 A Kasuwa

Majiyar ‘yan aware ta kasar Mali ta sanar da cewa wani hari da sojojin gwamnati su ka kai a arewacin kasar ya yi sanadiyyar kashe

Majiyar ‘yan aware ta kasar Mali ta sanar da cewa wani hari da sojojin gwamnati su ka kai a arewacin kasar ya yi sanadiyyar kashe mutane 18 a arewacin kasar Mali, sai dai sojojin gwamnatin ta ce, ‘yan aware ta kai wa hari.

Kungiyar Azbinawa ‘yan aware ta ce sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ne a garin Lerneb mai nisan kilo mita 50 daga birnin Timbuktu, a ranar Litinin da ta gabata kuma bayan mutane 18 da su ka kwanta dama, wasu 7 sun jikkata.

Kungiyar ta Azbinawa ta bayyana abinda ya faru da cewa; “Dabbanci” ne irin na zamanin jahiliyya.

Sai dai sojojin gwamnatin kasar ta Mali sun wallafa a shafinsu na X cewa; sun kai harin ne akan wata  tunga ta  ‘yan ta’adda tare da kashe 11 daga cikinsu.

Fiye da shekaru  10 kenan kasar ta Mali tare da makwabtanta, Burkina Faso da Nijar suke  fada da  kungiyoyi masu dauke da makamai da su ka hada al’ka’ida da kuma “Da’esh”.

Bayan juyin mulkin da aka yi a cikin kasashen uku, da korar sojojin Faransa, kasar ta Mali ta gayyato mayakan kungiyar “Wagner”  daga kasar Rasha, domin taya ta fada da masu dauke da makaman.

Sai dai a wasu lokutan ana samun kuskure irin wannan da wajen kai wa masu dauke da makamai hari, ake kai wa fararen hula.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments