Harin da Isra’ila ta kai ya kashe Falasdinawa 9 a arewacin Gaza

Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da

Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da ‘yan jarida uku a cikin gida, in ji ma’aikatan lafiya.

An kai harin ta sama a wata mota a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin yau Asabar.

A cewar likitocin, mutane da dama sun samu munanan raunuka, tare da jikkata a ciki da wajen motar.

“An kai shahidai tara zuwa asibiti, da suka hada da ‘yan jarida da dama da ma’aikata daga kungiyar agaji ta Al-Khair, sakamakon harin da aka kai wa motar da wani jirgi mara matuki a garin Beit Lahia, tare da luguden wuta a yankin,” in ji kakakin hukumar tsaron farar hula Mahmoud Bassal.

Shaidu da sauran ‘yan jarida sun ce mutanen da ke cikin motar na wata kungiyar agaji ve a garin, kuma Sun samu rakiyar ‘yan jarida da masu daukar hoto lokacin da harin ya same su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments