Harin da Isra’ila ta kai a garin Palmyra na Syria ya kashe mutane 36

Rahotanni na nuni da cewa wani hari da Isra’ila ta kai kan birnin Palmyra mai tarihi a kasar Siriya ya kashe mutane 36 tare da

Rahotanni na nuni da cewa wani hari da Isra’ila ta kai kan birnin Palmyra mai tarihi a kasar Siriya ya kashe mutane 36 tare da raunata fiye da 50.

Harin dai an kai shi ne kan wasu gine-gine da kuma wani yanki na masana’antu, in ji kamfanin dillancin labaran kasar Syria SANA.

Isra’ila ta kwashe shekaru tana kai hare-hare kan a sassa daban daban na Siriya amma ta kara kai hare-hare tun ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Tsohon birnin Palmyra yana cikin jerin wurare masu tarihi na duniya dake karkashin hukumar UNESCO.

Mayakan kungiyar da aka fi sani da ISIL (ISIS) ne suka kwace shi a shekarar 2015 kuma an lalata wani bangarensa kafin sojojin Syria su kwato shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments