Bayanai daga Afghanistan na cewa, ministan kula da ‘yan gudun hijira na gwamnatin, Khalil Haqqani ya mutu sakamakon fashewar wani abu a cikin hedkwatar ma’aikatar da ke tsakiyar birnin Kabul.
Haqqani, “ya yi mutu tare da wasu abokan aikinsa,” kamar yadda wani jami’in gwamnatin Taliban ya shaida wa AFP.
Kawo yanzu dai ba a bayyana ko su waye suka kai harin ba.
Khalil Haqqani ya zama minista a gwamnatin rikon kwarya ta Taliban bayan da sojojin Amurka suka fice daga kasar a shekara ta 2021.
Haqqani mai kula da matsalar ‘yan gudun hijira da ke shigowa Afganistan, Ya kuma kasance kawun Sirajuddin Haqqani, ministan cikin gida na yanzu.
Wani babban jami’i a ma’aikatar harkokin cikin gida ya shaidawa CBS News cewa an kashe Haqqani a wani harin kunar bakin wake tare da akalla wasu abokansa hudu.
Daga bisani mai magana da yawun kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid ya tabbatar da mutuwar Haqqani a harin tare da dora alhakinsa kan kungiyar Daesh a Afganistan.
Tun bayan da Taliban ta koma kan karagar mulki, an kashe wasu manyan shugabanninta da suka hada da gwamnonin larduna da kwamandoji da malaman addini, galibi a hare-haren da ‘yan ta’addar Dash suka dauka.
Har zuwa lokacin fasara wadanan labaranb babu wani ko wata kungiya data dauki alhakin fashewar.