Search
Close this search box.

Hare-haren Isra’ila Sun Yi Ajalin Falasdinawa 20 A Ranar Laraba

Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 20 ne sukayi shahada wasu kuma da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin

Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 20 ne sukayi shahada wasu kuma da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin na Gaza.

Mutum bakwai ne suka mutu sakamakon harin bam da Isra’ila ta kai kan wani gida da ke sansanin Nuseirat.

A Khan Younis, Falasdinawa hudu ne suka mutu a wani harin bam da Isra’ila ta kai kan wani gida inda ta kashe Falasdinawa biyu tare da raunata wasu a garin Bani Suhaila da ke gabashin birnin.

Falasdinawa uku ne suka mutu wasu kuma suka jikkata a wani samame da aka kai a wani gida da ke sansanin Al-Maghazi.

Falasdinawa biyu ne suka mutu wasu kuma suka jikkata sakamakon wani harin bam da aka kai a wani gida da ke yankin aikin Beit Lahia da ke arewacin Gaza.

Har ila yau, an kai hare-hare a yankunan Rafah, Al-Sabra, da Al-Zeitoun a cikin birnin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments