Hare-haren Isra’ila Sun Kashe Karin Mutane 50 A Gaza

Hukumomin lafiya a Gaza sun ce adadin Falasdinawa da sukayi shahada a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya kai 44,758 a sanadin hare-haren

Hukumomin lafiya a Gaza sun ce adadin Falasdinawa da sukayi shahada a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya kai 44,758 a sanadin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa.

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fada a yau Litinin cewa mutane 50 ne suka mutu a cikin sa’o’I da suka gabata sannan wasu 84 suka jikkata yayin wasu jerin hare-haren sojojin Isra’ila uku a yankin.

Wani harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza a safiyar Litinin ya kashe mutane uku, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa masu aiko da rahotanni..

Tsawon kwanaki 65 kenan da Isra’ila ta killace Jabalia, inda aka hana dubban Falasdinawa samun abinci da ruwan sha, lamarin da ya sanya da dama cikin yunwa.

A cikin dare kuma, wani hari da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Rafah, ya kuma kashe mutane 10 a lokacin da suka yi jerin gwano domin sayen gari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments