Hannayen jarin Starbucks da McDonald’s sun yi kasa bayan yin  kira da a kaurace musu

Alkaluma sun nuna cewa kauracewa kamfanonin da ke goyon bayan gwamnatin Isra’ila ya haifar da raguwar darajar hannayen jarin wasu manyan kamfanoni biyu na Amurka,

Alkaluma sun nuna cewa kauracewa kamfanonin da ke goyon bayan gwamnatin Isra’ila ya haifar da raguwar darajar hannayen jarin wasu manyan kamfanoni biyu na Amurka, Starbucks da McDonald’s.

Rahotanni da dama sun tabbatar da cewa, McDonald na shirin rage farashin abincinsa zuwa dala 5 a gidajen cin abinci da yake mallaka a kasar Amurka domin samun karin kwastomomi bayan hasarar da aka samu sakamakon kauracewa kayayyakin kamfanonin da ke goyon bayan gwamnatin yahudawan sahyoniyawa a duniya.

A cewar wani rahoto da Bloomberg ta fitar, tallace-tallacen kamfanin ya ragu a ‘yan watannin nan, yayin da ake ci gaba da yin kisan kare dangi a yankin zirin Gaza, kuma a lokaci guda kuma ya samu raguwar karuwar tallace-tallacen da yake yi a duniya a wata na hudu a jere.

Shafin Bloomberg ya tabbatar da cewa tallace-tallacen kamfanin ya ragu sosai tun a watan Oktoban da ya gabata, sakamakon zargin da ake ma kamfanin na goyon bayan sojojin Isra’ila da suke yin da kisan kiyashi kan fararen hula a zirin Gaza.

A daya hannun kuma, wani kamfanin na Amurka Starbucks ya shaida daya daga cikin makwanni mafi muni a tarihinsa, yayin da hannun jarin kamfanin ya fuskanci koma baya mafi muni  tun shekara ta 2000.

Kamfen na kaurace wa kayayyakin gwamnatin sahyoniya  da kayayyakin kasashe da kamfanonin da ke hada kai da ita a duniya, na amfani da wata manhaja wato app na New Zealand da aka samar  don sauƙaƙe gano wuraren cin abinci da kayayyakin halal, wanda yana taimakawa wajen gano kayayyakin kamfanonin da suke da alaka da Isra’ila domin kaurace musu.

McDonald’s, Starbucks, giant Mondel’s, kayan kamshi na Jo Malone da Johnson & Johnson suna cikin kamfanonin duniya da ke cikin jerin da kamfen din ya shafa kai tsaye.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments