Hamas: Za A Yi Musayar Fursunoni Kamar Yadda Aka Tsara

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa.

A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da  cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara.

Tashar talabijin din Aljazira ta ambato majiyar kungiyar ta Hamas tana cewa, tawagarta tana tattaunawa d a Masar da Katar  a matsayinsu na masu shiga tsakani musamman akan yadda za a kai wa mutanen Gaza, hadaddun matsugunan da za su rayu a ciki da kuma magunguna da sauran bukatu na  kiwon lafiya na gaggawa. Haka nan kuma an warware matsalar kai kayan agaji da za a bari su rika shiga cikin Gaza ba tare da kakkautawa ba.

Wasu daga cikin matsalolin da aka warware sun hada bayar da damar shigar da manyan kayan aiki da motocin buldoza na kwashe baraguzai, da shigar da makamashi, da kuma  magunguna.

Sanarwar da kungiyar ta Hamas ta wallafa a shafinta na “Telegram” ta ambato masu shiga tsakani da su ne kasashen Masar da Katar suna cewa, za su sa ido domin ganin cewa ana aiki da abubuwan da aka yi yarjejeniyar akansu.

Wannan matakin na kungiyar Hamas, ya zo ne bayan da a kwanaki kadan da su ka gabata ta sanar da dakatar da batun sakin fursunonin har illa masha Allah, saboda yadda HKI take take sharuddan yarjeniyar da aka cimmawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments