Hamas : Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Da Isra’ila Na Cikin Hadari”

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,” Bassem Naïm, ne

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,”

Bassem Naïm, ne wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar, ya bayyana hakan ga kamfanin AFP, yayin da tattaunawar da ake yi kan mataki na biyu na tsagaita bude wuta, da ya kamata a fara ranar Litinin, ke ja da baya ba kamar yadda aka fara ba inji shi.

Da yake zargin Isra’ila da “jinkiri” wajen aiwatar da kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta na makonni shida, wanda ya fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, Bassem Naim ya yi gargadin cewa wannan lamarin ya jefa yarjejeniyar cikin hadari kuma zata iya haifar da rugujewarta.

Kawo yanzu dai ba a bayar da cikakken bayani kan ci gaban tattaunawar da ake yi a mataki na biyu ba, da nufin ganin an sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma kawo karshen yakin.

Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183 yau Asabar, a madadin wasu mutanenta uku daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da suka cimma.

Tun bayan fara tsagaita wutar, an sako wadanda ake garkuwa dasu 18 da da fursunonin falasdinawa 582.

Kashi na farko na yarjejeniyar, wanda zai dauki tsawon makonni shida, ya tanadi mikawa Isra’ila jimillar mutane 33 da aka yi garkuwa da su, ciki har da akalla takwas da suka mutu, a madadin Falasdinawa 1,900.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments