Hamas Tayi Allawadai Da Gwamnatin Mahmud Abbas Dangane Da Zubar Da Jinin Falasdiawa A Jinin

Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza na kasar Falasdinu, ta yi allawadai da gwamnatin Falasdinawa ta Mahmood Abbas kan zubar da jinin Falasdinawa

Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza na kasar Falasdinu, ta yi allawadai da gwamnatin Falasdinawa ta Mahmood Abbas kan zubar da jinin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar ta na fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa Labaran da suke isa wajenta sun nuna cewa yansanda Mahmood Abbas suna kama hatta Falasdinawa wadanda aka kawo su asibiti a yankin saboda raunukan da sojojin yahudawa suka ji masu a Jenin.

Kungiyar ta ce, wannan ya nuna cewa gwamnatin Mahmood Abbas ta hada kai da sojojin HKI don cutar da falasdinawa masu gwagwarmaya da ita.

Banda haka yansandan gwamnatin Mahmood Abbas sun wuce iyaka, saboda hada kai ha gwamnatin yahudawa, wajen cutar da Falasdinawa masu gwagwarmaya a yankin yamma da kogin Jordan.

Daga karshen kungiyar ta bukaci dukkan kungiyoyin Falasdinawa su fito dan fuskantar sojojin yahudawan da kuma na Mahmoos abbas saboda yadda suka hada kai don cutar da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments