Hamas : Tattaunawar sulhu ba ta da wani tasiri a halin da ake ciki

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa tattaunawar sulhu a Gaza ba ta da wani tasiri a wannan mataki. Ofishin kungiyar, ya yi kira

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa tattaunawar sulhu a Gaza ba ta da wani tasiri a wannan mataki.

Ofishin kungiyar, ya yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba kan gwamnatin Netanyahu don kawo karshen laifukan yunwa, kishirwa da kisan kai a Gaza, in ji wani babban jami’in kungiyar.

Halin da ake ciki a Gaza ya kai intaha inji kungiyoyin kasa da kasa.  

A wani rahoto data fitar a baya baya nan kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta yi gargadi kan halin da ake ciki a zirin fiye da na watanni 19 da suka gabata.”

kungiyar ta jaddada cewa “mafi yawan jama’a na yankin na fuskantar matsananciyar hadarin yunwa.”

Sama da mutane miliyan daya da suka rasa matsugunansu a zirin Gaza ba su da damar samun ababen bukatuwa na yau da kullun.

Tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023, lokacin da gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a kan zirin Gaza, an kashe Falasdinawa sama da 52,535 tare da jikkata wasu fiye da 118,491 galibi mata da kananan yara.

A cikin watan Janairu, kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da gwamnatin mamaya ta Isra’ila sun amince da shirin tsagaita wuta na matakai uku, wanda ya fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, saidia daga bisani Isra’ila ta fi fatali da shi ta koma kai hare-haren ta a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments