Hamas Ta yi Watsi Da Batun Tura Sojojin Kasashen Waje Zuwa Gaza

Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas Musa abu marzuk ya shaidawa gidan talabijin din Aljazeera cewa  sun yi watsi da batun tura

Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hamas Musa abu marzuk ya shaidawa gidan talabijin din Aljazeera cewa  sun yi watsi da batun tura dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa yankin Gaza wadanda zasu yi aiki a madadin sojojin mamayar Isra’ila

Yace ba zamu taba amincewa da aikewa da sojojin da za su zama madadin sojojin Isra’ila a gaza ba,

Wannan bayanin ya zo ne bayan da kasar Amurka ta fitar da wani daftarin kuduri a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya dake bukatar kafa dakarun tababtar da zaman lafiya na wucin gadi a yankin Gaza, akalla na shekaru 2 adaidai lokacin da falasdinawa ke fargabar tsoma bakin kasashen waje a yankin,

Rahotanni da aka fitar ya nuna cewa kasashen Amurka, Turkiya, Qatar da kasar Masar ne za su kafa dakarun tabbatar da zaman lafiya a Gaza, kasashen da suka jagorancin tattaunawar dakatar da bude wuta tsakanin isra’ila da Hamas tun a watan daya gabata

Ana sa bangaren Musa Abu Marzuk ya kara da cewa zai zama lamari ne mai wahalar gaske kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya ya kafa dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar a yankin Gaza kamar yadda Amurka ta tsara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted