Hamas Ta Yi Tir Da Shawarar Shugaban Amurka Ta Kwashe Falasdinawa Daga Gaza

Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da mazauna Gaza zuwa kasashen Masar da Jordan dake makwabtaka da ita.

Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da mazauna Gaza zuwa kasashen Masar da Jordan dake makwabtaka da ita.

A cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaban kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya yi tir da irin wadannan shawarwari a matsayin “abin dariya kuma maras amfani,” yana mai cewa, “Abin da mamayar Isra’ila ta kasa cimma da karfi, ba zai samu ta hanyar makircin siyasa ba.”

Abu Zuhri ya kara da cewa, “Sanarwar da Amurka ta nanata na raba Falasdinawa da gidajensu da nufin sake gina yankin zirin Gaza na nuni da yadda kasar ke da hannu wajen aikata laifukan da suka shafi yanki.”

Kana, ya yi gargadin cewa, “aikin kwashe mazauna Gaza” wani makirci ne na kara hargitsi da tashin hankali a yankin.

A ranar 25 ga watan Janairu ne dai Trump ya gabatar da wannan tsari mai cike da cece-kuce na kwashe Falasdinawa daga Gaza zuwa Masar da Jordan, wanda kasashen biyu suka ki amincewa da shi matuka.

Shi dai Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada kiransa ga kasashen Masar da Jordan domin su karbi Falasdinawan Gaza da suka rasa matsugunansu, duk da cewa kasashen Larabawan biyu sun yi watsi da shawararsa da ke cike da ce-ce-ku-ce.

Haka su ma kasashen Qatar, UAE da kuma Saudiyya sun yi fatali da shawarar da Trump ya bayar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments