Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye

Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi Allah wadai da sabbin gine-ginen mastugunnan yahudawa yan share wuri zauna guda 764 da isra’ila take ginawa a gabar

Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi Allah wadai da sabbin gine-ginen mastugunnan yahudawa yan share wuri zauna guda 764 da isra’ila take ginawa a gabar yammacin kogin jodan , kuma ta bayyana shi a matsayin wani shiri na mayar da yankin ya koma na yahudawa.

Wannan matakin yana nuna irin yadda isra’ila ta ke ci gaba da fadada gine-ginenta a yankun da aka dauki dogon lokaci ana takaddama akai, kuma babbar barazana ce ga yankunan dake ciki yankunan falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan,

Siyasar ci gaba  da Gine gine na isra’ila ya kara sauri a yan shekarun nan duk da nuna rashin amincewa da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya nuna, kuma ya bukaci ta dakatar da dukkan gine-ginen da take yi domin ya sabama dokokin kasa da kasa,

Kungiyoyin falasdinawa sun yi gargadin cewa  ci gaba da kwace filaye da nufin samar da cikakken iko ga Isra’ila da kuma korar yan asalin kasar,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted