Hamas ta yi tir da matakin Isra’ila na shirin takura masu ibada a masallacin Quds

Kungiyar ​​Hamas ta yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na sanya takunkumin hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.

Kungiyar ​​Hamas ta yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na sanya takunkumin hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi ishara da umarnin da ‘yan sandan Isra’ila suka bayar na ba wa masu ibada 10,000 kawai damar gudanar da sallar Juma’a a harabar masallacin Al-Aqsa, tana  mai cewa matakin wani lamari ne mai matukar  hadari da ke da nufin tauye ‘yancin addini.

Hamas ta ce, umarnin ‘yan sandan Haramtacciyar Kasar Isra’ila  cin zarafi ne  ga dukkan ka’idoji, yarjejeniyoyin da kuma dokoki na kasa da kasa, sannan kuma hakan tsokana ce kai tsaye ga musulmi.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa, irin wadannan tsare-tsare ba za su yi tasiri wajen sauya asali da tarihin masallacin Al-Aqsa ba.

Bugu da kari kuma Hamas ta dora alhakin abin da hakan zai iya haifarwa a kan gwamnatin yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayin kin musulunci.

Daga karshe kungiyar Hamas ta yi kira ga kungiyar hadin kan kasashen musulmi da kasashen duniya da su dauki tsauraran matakai domin dakile wannan mataki na keta alfarmar  masallacin Al-Aqsa, da kuma tabbatar da cewa al’ummar Palastinu na gudanar da ibadarsu cikin ‘yanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments