Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa, Hamas, ta yi kakkausar suka kan rufe makarantu guda 6 na MDD da Isra’ila ta yi a yammacin gabar kogin Jordan, tare da bayyana hakan a matsayin keta dokokin kasa da kasa
ranar Alhamis 8 ga watan Mayu, Hamas ta bayyana cewa harin da aka kai kan makarantun hukumar agaji ta MDD UNRWA da ke birnin Quds da aka mamaye, da kuma rufe su da aka yi bayan korar dalibai da malamai da aka yi, ya zama harin kai tsaye ga daukacin tsarin MDD da cibiyoyinta.
Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, irin wadannan matakai na aikata laifuka wani bangare ne na yakin da gwamnatin Isra’ila ke yi da wanzuwar Falasdinu da kuma asalinsu.
Don haka kungiyar ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da dukkanin hukumomin kasa da kasa da abin ya shafa da su dauki matakai na gaggawa don kawo karshen cin zarafi da gwamnatin Isra’ila ke yi tare da tabbatar da mayar da yara Falasdinawa sama da 800 zuwa ajujuwa.
Tuni dai kwamishinan hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa makarantun hukumar, yana mai tunatar da cewa wadannan cibiyoyi na da kariya ce ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma rufe su cin zarafin yara ne da kuma ‘yancin samun ilimi.