Hamas Ta Yi Maraba Da Shirin Sake Gina Gaza Da Taron Kasashen Larabawa Ya Gabatar

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da shirin sake gina Gaza na Masar da aka amince da shi a wani taron gaggawa na

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da shirin sake gina Gaza na Masar da aka amince da shi a wani taron gaggawa na kasahen Larabawa da aka yi a birnin Alkahira.

Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, taron na birnin Alkahira ya nuna wani muhimmin mataki na daidaita alaka tsakanin Larabawa da Musulunmi da Falasdinu, musamman a ci gaba da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, da yammacin kogin Jordan da kuma al-Quds.

Kungiyar ta yabawa shugabannin kasashen Larabawa da suka yi watsi da yunkurin raba Falasdinawa da kasarsu, tana mai danganta da sako mai cike da tarihi.

Hamas ta yi marhabin da kiran tana mai bayyana shi a matsayin “tsari mai inganci don mai da Isra’ila saniyar ware tare da matsa mata lamba ta bi dokokin kasa da kasa.”

Hamas ta jaddada bukatar aiwatar da shirin sake gina yankin, da tabbatar da isar da kayan agaji cikin gaggawa, da kuma yin aiki don tabbatar da tsagaita bude wuta da kuma tabbatar da an bi sharuddan da aka cimma.

A taron da suka gabatar ne Shugabannin kasashen Larabawa suka amince da shirin sake gina Gaza, wanda ya tabbatar da kin amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu “a karkashin kowane irin yanayi.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments