Hamas Ta Yi Bukaci A Hukunta HKI Akan Rusa Asibitoci

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana cewa, laifukan da HKI take tafkawa akan jami’an kiwon lafiya suna da bukatar duniya ta yunkura cikin gaggawa.

Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana cewa, laifukan da HKI take tafkawa akan jami’an kiwon lafiya suna da bukatar duniya ta yunkura cikin gaggawa.

A wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar a jiya Asabar wacce ta kunshi wannan bayanin ta kuma ce; Sojojin mamaya suna ci gaba da rusa sauran cibiyoyin kiwon lafiya da su ka saura a yankin Gaza,haka nan kuma kai wa likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya hari.

Kungiyar ta Hamas ta bayyana abinda HKI take yi a karkashin ci gaba da rusa duk wani abu mai amfani a yankin Gaza.

Wani sashe na sanarwar kungiyar ta Hamas ya kuma ambaci cewa; Ya zuwa yanzu adadin likitoci da ma’aiaktan kiwon lafiya da HKI ta kashe a Gaza sun haura 1,700,kuma tana tsare da wasu da adadinsu ya kai 400.”

Kungiyar gwgawarmayar ta Falasdinawa ta kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su yunkura cikin gaggawa domin taka wa HKI birki akan laifukan da take tafkatawa cikin ganganci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments