Hamas Ta Taya Siriyawa Murnar Hambarar Da Assad

A cikin wata sanarwa da kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu ta fitar a shafinta na intanet, Hamas ta ce: Muna taya ‘yan’uwa al’ummar Siriya murnar samun

A cikin wata sanarwa da kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu ta fitar a shafinta na intanet, Hamas ta ce: Muna taya ‘yan’uwa al’ummar Siriya murnar samun nasarar cim ma burinsu na samun ‘yanci da adalci.

“Muna kira ga dukkan bangarorin al’ummar Siriya da su hada kai su karfafa kasarsu da kuma samun waraka daga abubuwan da suka gabata.

Muna kuma kira ga al’ummar Siriya da su shawo kan kalubalen da suke fuskanta ta yadda za su ci gaba da rawar da suke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu da kuma tsayin daka,” in ji kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a cikin wata sanarwa da ta fitar yau.

Daga karshe kungiyar ta yi Allah wadai da zaluncin da gwamnatin mamaya ke yi wa yankunan Siriya.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments