Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta mika gawawwakin mutum hudu ‘yan Isra’ila ga kungiyar agaji ta Red Cross.
Mutanen dai Isra’ila ta kasha su a cikin wadanda Hamas ta yi garkuwa da su lokacin kai hare-hare a Gaza.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta nufi wani wuri a Gaza domin karbar gawawwakin ‘yan Isra’ilan hudu da aka shirya mikawa karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kamar yadda kafafen yada labaran Isra’ila suka rawaito.
Dakarun na Hamas sun mika gawawwakin a Khan Younis da ke kudancin birnin Gaza.