Hamas Ta Godewa Iran Da Kungiyoyin Gwagwarmaya Bayan Nasarar Tsagaita Wuta

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinjinawa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza biyo bayan cin nasara kan gwamnatin Isra’ila a yakin da aka shafe watanni

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinjinawa Falasdinawa a yankin Zirin Gaza biyo bayan cin nasara kan gwamnatin Isra’ila a yakin da aka shafe watanni 15 ana yi na kisan kare dangi.

Khalil al-Hayya, mataimakin shugaban ofishin siyasa na kungiyar ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar jim kadan bayan cimma yarjejeniyar.

Ya godewa Jamhuriyar Musulunci, kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, Dakarun Yeman, da ‘yan gwagwarmaya a Iraki.

Jami’in ya yaba wa kungiyar Hizbullah wacce daruruwan mambobinta sukayi shahada, da suka hada da shugabanni da mayaka, a kan hanyar [yanto birnin Qudus mai tsarki] karkashin jagorancin babban sakatarenta Sayyed Hassan Nasrallah.”

Jami’in yana mai yabawa dubban hare-haren ramuwar gayya da kungiyar, da sojojin Yemen, da mayakan sa kai na Iraki suka kaddamar domin mayar da martani ga mummunan harin soji da gwamnatin Isra’ila ke kai wa Gaza da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Lebanon.

Ya kuma gode wa mayakan gwagwarmayar Falasdinawa a yammacin gabar kogin Jordan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments