Hamas Ta Dakatar Da Sakin ‘Yan Isra’ila Sai Abinda Hali Ya Yi

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinkirta sakin sauren karin ‘yan Isra’ila da take garkuwa dasu “har sai an ga abinda hali ya yi”, saboda

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinkirta sakin sauren karin ‘yan Isra’ila da take garkuwa dasu “har sai an ga abinda hali ya yi”, saboda keta dokar da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta a Gaza.

Sanarwar da bangaren soji na Hamas ta fitar bakin kakakinta Abu Obeida, ta bayyana cewa ‘’fiye da mako uku makiya sun gaza wajen cika yarjejeniyar da suka cimma’’.

Hamas ta ce ‘’sakin karin wasu yahudawa na ranar Asabar 25 ga wata an jingine shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran makiya su mutunta yarjejeniyar da aka fara aiwatarwa makkonin da suka gabata.

Tuni dai Isra’ila ta mayar da martani dangane da sanarwar ta Hamas inda a wata sanarwa da ministan tsaron kasar ya fitar ta ce ” sanarwar dakatar da sakin wadanda Hamas ke garkuwa da su ya saba yarjejeniyar tsagaita cimma wutar da ta musayar fursunoni.

Ministan tsaron Isra’ilar, Israel Katz, ya ce “ya bai wa dakarun IDF umarnin kasancewa cikin ko-ta-kwana dangane da duk wani abu da ka iya biyo ba a Gaza domin kare al’umma, ya kara da cewa “Ba za mu bari a maimaimata abin da ya faru ranar 7 ga watan Oktoba ba.

Shi kuwa shugaban Amurka Donald Trump, ya ba da shawarar soke yarjejeniyar Gaza yayin da Hamas ta dakatar da sakin fursunonin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments