Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta sanar da fara shawarwarin tsagaita wuta a mataki na biyu tsakaninta da Isra’ila.
Kakakin Abdul Latif al-Qanou ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a kafar sadarwar zamani.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a tashar ta Telegram mai magana da yawun kungiyar Abdel Latif al-Qanoua ya zargi Isra’ila da “jinkirta aiwatar da ka’idojin jinƙai a yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dakatar da aiwatar da hukuncin kisa.”
Ya ce har yanzu kungiyar Falasdinu ta damu da batutuwa da dama da suka hada da matsuguni ga mutanen Gaza, da kuma kayan agaji da kuma kokarin sake gina yankin.
Al-Qanou ya kuma zargi Isra’ila da “katse” ka’idojin jin kai da ke kunshe cikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da jinkirta” aiwatar da su.
Isra’ila ta ce ta aike da wata tawaga domin tattaunawa a mataki na gaba a tsagaita wuta mai rauni da kungiyar Hamas, wanda ke nuni da yiwuwar samun ci gaba gabanin ganawar firaminista Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Donald Trump a ranar Talata.
Bayanai sun ce Isra’ila ta ci gaba da keta yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare Gaza.
Isra’ila ta kama Falasdinawa akalla 380 tun bayan tsagaita bude wuta a Gaza inji kungiyoyi masu zaman kansu akasarinsu matasa a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu.