A wani bayani da kungiyar Hamas din ta fitar tayi tir da Israila kan yanayin da gawarwarakin da ta bata na palasdinawa dake hannunta, inda aka ga alamomi na Azabtarwar ajikinsu da kuma cire wasu sassan jikinsu don haka ta yi kara da a kafa kwamitin bincike na kasa da kasa kan halin rashin dan adamta da isra’ilan ta nuna kan gawarwakin.
Ta ce yin amfani da hanyoyi daban daban wajen Azabtarwa yana haifar da damuwa sosai kuma ya taka dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Janeva, kuma wadannan ayyukan daidai suke da kisan kiyashi kan alummar falasdinu,
Wasu kungiyoyin sun mika batun ga kwamitin kula da hakokin dan adam na majalisar dinkin duniya domin yin matsin lamba kan isra’ila don a gudanar da bincike,
Kungiyar hamas ta ce tana kira ga kunyoyin kare hakkin bil adama da na kasa da kasa da su rubuta wannan abin da ya faru, kuma a gudanar da bincike na gaggawa tare da gurfanar da shuwagabannin isra’ila kan laifukan cin zarafin bil adama da ba’a taba ganin irinsa ba a tarihi na zamani.