Hamas ta amince da daftarin zaman lafiya na Trump

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta amince da daftarorin zaman lafiya da shugaba Donald Trump ya gabatar, wanda ganin zai kai ga kawo karshen yakin

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta amince da daftarorin zaman lafiya da shugaba Donald Trump ya gabatar, wanda ganin zai kai ga kawo karshen yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Zirin.

A wata sanarwa da ta fitar kungiyar “ta bukaci janyewar dukkan sojojin Isra’ila, sannan ta saki dukkan Isra’ilawan da suke tsare a hannunta, masu rai da matattu.”

Kungiyar, ta kuma ce sakin zai faru “idan har an tabbatar da yanayin tsarin musayar.”

Don haka, kungiyar ta ce a shirye take ta shiga tattaunawa da masu shiga tsakani domin cimma manufar.

Haka zalika, Hamas ta ce ta amince da mika ragamar mulkin zirin ga wata hukumar Falasdinu mai cin gashin kanta.

Duk da haka, kungiyar ta bayyana cewa sauran tanade-tanaden da aka ambata a cikin shirin na Trump dole ne a amince da su “ta hanyar cikakken tsarin kafa kasar Falasdinawa wanda Hamas za ta kasance a cikinta kuma za ta ba da gudummawa.”

Tuni dai shugaba Trump wanda ya gabatar da daftarorin guda 20 a farkon makon nan, ya wallafa a shafinsa na Truth cewa Hamas a shirye take don samun zaman lafiya mai dorewa, ya kuma shaidawa Isra’ila cewa dole ne ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted