Hamas, Da OIC Sun Yi Tir Da Farmakin Isra’ila A Tulkaram

Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta yi allawadai da kutsawar da firai ministan HKI da kuma ministan

Kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, a kasar Falasdinu da aka mamaye, ta yi allawadai da kutsawar da firai ministan HKI da kuma ministan yakin sa Israel Kantz zuwa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram a yankin yamma da kogin Jordan.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin HKI sun kutsa cikin sansanonin yan gudun hijira na Palasdinawa a Tulkaram da kuma Jenin tana rusa gidajen falasdinawa tana kuma kora da kuma kashe wadanda suka samu a cikin gidajen nasu.

A wani labarin kuma kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta yi allawadai da rushe-rushen gidajen da gwamnatin HKI take yi a yankin yamma da kogin Jordan.  Kungiyar ta yi kira da kasashen duniya su sa baki don dakatar da kashe Falasdinawa da kuma korarsu daga gidjensu da kuma rusa wasu gidajen.

Kungiyar ta kara da cewa kutsawa cikin sansanin yan gudun hijira na Tulkaram ci gaba da zaluncin da takewa Falasdinawa a tsawon shekaru 76  da suka gabata. Har’ila yau ministan harkokin wajen Falasdinawa ya yi tir da Natanyahu da kuma Kanzt kan abinda suke aikatawa a garin Tulkaram. Inda suke son korar faladinawa kimani 40000 da suke rayuwa a sansanin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments