Hadakar Kasashen Sahel na AES, sun yi ban kwana da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO a hukumance bayan shekaru 50 na kasancewa mamba a cikinta.
Ya zuwa wannan Laraba, 29 ga Janairu, bangarorin biyu sun raba gari duk da cwa kungiyar ta ECOWAS ta baiwa kasashen wa’adin watannin shida ko zasu canza ra’ayi.
Kasashen na Mali, Nijar da kuma Burkina Faso sun ce bakin alkalami ya riga fa ya bushe.
A jiya Talata al’umomin kasashen guda uku sun gudanar da gangami da jerin gwano na nuna murnar ficewa daga kungiyar da suka ce ta zama ‘yar amshin shatan kasashen yamma musamman faransa wacce ta yi musu mulkin mallaka.
Haka zalika a wannan Larabar ce kasashen uku zasu kaddamar da fasfonsu, amma sun ce masu rike da fasfon Ecowas zasu ci gaba da amfani da shi, kuma sauren al’umomin kasashen ECOWAS zasu ci gaba da shige da fice cikin ‘yanci.
Matakin Kasashen na AES bai shafi kungiyar UEMOA ta kasashe guda 8 da ke anfani da kudin bai daya na sefa ba, Don haka ‘yancin zirga-zirgar jama’a da kayayyaki ya kasance tabbatacce a wannan yanki wanda ya hada kasashen Ivory Coast, Senegal da Benin.
A ranar 28 ga watan Janairu 2024, kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar suka ba da sanarwar ficewa daga kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka. Hakan ya biyo bayan kirkirar kungiyar AES na Kawancen Sahel a ranar 6 ga watan Yulin 2024.