Gwamntin Nijeriya tace Za ta Kare Sojojinta Da Ke Bakin Aiki

Ministan Tsaron nageriya, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa tare da shugabancin rundunar soji za su kare kowane jami’i da ke bakin aikinsa bisa

Ministan Tsaron nageriya, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa tare da shugabancin rundunar soji za su kare kowane jami’i da ke bakin aikinsa bisa doka.

Badaru ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ma’aikatar tsaro kan bikin tunawa da Sojojin Nijeriya na shekarar 2026, wanda aka gudanarwa a Cibiyar Tsaron Ƙasa (National Defence College), Abuja, a ranar Laraba.

Kalamansa na zuwa ne bayan rikicin da ya barke a bainar jama’a tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojan ruwa, Laftanar A. M. Yerima, kan wani fili da ke Abuja da ake zargin mallakar tsohon Shugaban Rundunar Sojan Ruwa, Vice Admiral Zubairu Gambo (mai ritaya) ne.

Ya ce: “A Ma’aikatar Tsaro, da ma rundunonin sojoji gaba daya, za mu ci gaba da kare jami’anmu da ke aikin doka. Muna bincike kan wannan lamari, kuma muna tabbatar da cewa duk jami’in da yake aikinsa bisa doka, za a kare shi. Ba za mu bari wani abu ya same shi  ba matukar yana aikinsa yadda ya kamata kuma yana yin aikinsa sosai.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted