Gwamnatin Sudan Ta Yi Allah Wadai Da Sabbin Takunkuman Da Amurka Ta Kakaba Mata

Gwamnatin Sudan ta bayyana cewa: Sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata, bakar siyasa ce ta nemen bata mata suna A cikin wata sanarwa da

Gwamnatin Sudan ta bayyana cewa: Sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba mata, bakar siyasa ce ta nemen bata mata suna

A cikin wata sanarwa da gwamnatin Sudan ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakaba mata sabbin takunkumai, tana mai bayyana hakan a matsayin maimaita kura-kurai irin na baya kan yadda gwamnatocin Amurka suka tafiyar da harkokin Sudan cikin kura-kurai.

Sanarwar ta kara da cewa: “takunkuman da Amurka ta fitar, zarge-zarge ne da suke neman bata sunan kasar da murguda gaskiyar lamari; inda ta ci gaba da bayyana cewa: “Amurka tana ci gaba da bin manufofin da ke kawo cikas ga hanyar da al’ummar Sudan ke bi wajen samun kwanciyar hankali da zaman lafiya.”

Gwamnatin Sudan ta jaddada cewa: “Takunkuman da Amurka ta kakaba wa sojojin ne bayan nasarorin da suka samu a fagen yaki da suka hada da sauya gaskiyar yakin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted