Mataimakin shugaban Majalisar Gudanar da Mulki a kasar Sudan ya sanar da rufe ƙofar tattaunawa da Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces
Shamsuddeen Al-Kabbashi mamba a majalisar gudanar da mulkin kasar Sudan, kuma mataimakin babban kwamandan hafsan hafsoshin sojin Sudan, ya sanar da cewa: An rufe duk wata tattaunawa tsakanin rundunar sojin Sudan da Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, yana mai jaddada matsayinsu kan zabin hanyar warware matsalar kasar ta hanyar nuna karfin soja.
Wannan ya zo ne a cikin jawabin da ya gabatar a yankin masana’antar sukari na jihar Sennar da ke shiyar kudu maso gabashin, inda ya jaddada cewa: Ba zai yiwu a tsagaita bude wuta ko sasantawa da Dakarun kai daukin gaggawa ba, yana mai jaddada yin kira ga Dakarun kai daukin gaggawa da su mika makamai tare da mika kansu ga jami’an tsaron kasar.
Al-Kabbashi ya kara da cewa: Hanyar siyasa ba ta da alaka da hanyar soji, yana mai jaddada cewa; Za a ci gaba da zabar hanyar magance matsalar kasar ta nuna karfin soja. Al-Kabbashi ya dora alhakin rugujewar masana’antar sukari ta Sennar da lalata ta akan Dakarun kai daukin gaggawa tare da rusa duk wasu ababen more rayuwa, yana mai daukan alkawarin sake gina masana’antar da kuma gyara abubuwan da suka lalace a ciki.